18 Faburairu 2026 - 18:10
Source: ABNA24
Yamen: Ansarullah Ta Yi Gargaɗi Ga Saudiyya

Wani memba na ofishin siyasa na ƙungiyar Ansarullah ta Yemen ya yi gargaɗi, yana mai nuni da matakan da Saudiyya ke ɗauka na nuna ƙiyayya ga ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: "Ali Al-Dailami" ya jaddada cewa: Jami'an Saudiyya na ci gaba da yunkuri na tunanin mamayar Yemen, kuma wannan manufar ta samo asali ne daga tunanin masu basu umarni na Amurka, domin suna ɗaukar Yemen a matsayin wani yanki da ke da tasiri a Saudiyya.

Ya ƙara da cewa: Hare-haren da ake kai wa Yemen da kuma killace wannan ƙasa ba su tsaya ba, sai dai sun ƙara tsananta, har suka mamaye rayuwar mutanen wannan ƙasar.

Al-Dailami ya bayyana cewa: Ba za mu iya ganin matsalolin tattalin arziki da na rayuwa na mutanen Yemen ba musa ido. Abubuwan da ɓangaren Saudiyya ke fakewa da shi zai haifar da sakamako masu haɗari, kuma haƙurin mutanen Yemen ba wai ba ya da iyaka ba ne.

Ya jaddada: Dole ne a dakatar da yiwa Yemen kawanya da kuma tsoma baki a harkokin cikin gida na wannan ƙasar kuma maƙiya dole ne su janye daga ƙasar Yemen. Harin Amurka kuma ya ta'allaka ne kan ƙara tsananta killace Yemen a fannin tattalin arziki. Muna ba wa Saudiyya shawara da ta yanke takamaiman shawara game da wannan batu kafin lamarin ya ta'azzara.

Your Comment

You are replying to: .
captcha